Prodigits |
! You are not logged in to Prodigits. Please register or login.
* Abbaatee1 > Topics
abbaatee
WAI SHIN ANA SCANNING NA CIKI
DA WAYAR HANNU?
Wannan wata tambaya ce da
wasu daga mabiya Duniyar Waya
suke yi min,domin suna cewa
sunga cewar anrubuta a wani
shafi, da cewar, '' Zaka iya
Scanning na ciki da wayar
hannu''
To wannan rubutu da kuka gani,
ba haka yake ba, domin ba'a gane
mace mai ciki ta wayar hannu, ko
kuma agano wata cuta ta hanyar
hada wayar da jikin mutum
domin agani wata cuta dake
damunsa.
X-RAY SCANNER
Tabbas akwai wannan
application din akan waya, kuma
yana yi akan duk wata waya mai
daukan application, domin akwai
karaminsa, akwai babba, akwai
na android, amma dai duk aikinsu
daya, babu wani daga ciki da zai
baka damar gane mace mai ciki.
Wannan applications an kirkiri na
waya ne dan jawo hankalin yara,
masu sha'awar likitanci, da
wadanda suke bangaren dansu
fahimci aikinsu cikin sauki, da
kwanciyar hankali.
Kuma shi wannan application
yana aiki ajikin mutum, amma
bayayi kamar asalin scanner,
domin shi wannan application
abinda aka dura masa su kadai
yake nunawa.
Misali idan kana da shi zaka ga ya
nuna maka
Kashin hannun hagu
Kashin hannun dama
Yatsun hannu ko kafa.
yana nuna hoton kai.
Yana nuna kafofin mutum
Akwai wanda yake nuna hoton
ciki.
Akwai mai nuna hoton yaro
aciki
Akwai mai nuna tsintsiyar
hannu
Akwai mai nuna bayan mutum.
Ds
Amma kasani duk wadannan
abubuwa acikinsa suke, koda
kuwa sama ka haska, to haka zai
nuna maka, amma za'a iya
yakarka da shi idan baka sanshi
ba, domin za'a iya karashi
ajikinka, kaga yana nuna wasu
abubuwa na daga jikin mutum,
amma bayayi.
Ai abu na farko camerar dake
jikin waya bata isa ta nuna
wadannan abubuwan ba, saboda
bata da nisan gano abu, sannan
bata yinkurin fitar da na boye,
balle wanda yake ciki.
Kai tsaye wannan magana ta
awun ciki da waya, ba gaskiya
bace, domin waya bata isa ta
auna ciki ba, sai dai wadanda
za'ayi nan gaba, amma yanzu
ba'ayi wannan wayar ba.
Kuma idan kai kana auna ciki da
wayarka, ga tambaya
1. Wacce irin waya ce dakai?
2. Wanne kamfani ne suka hada
wannan abun?
3. Waya kirkiri wannan software
din?
4. Yaushe ka fara amfani dashi?
5. Mutum nawa ka auna ka gano
cutaajikinsu?
Wadannan tambayoyi sune
yakamata, kayiwa wanda ya ce
maka ana auna ciki da wayar
hannu.
Kai babbar tambaya waya kirkiri
software din, domin kana binciko
sunansa zaka ga duk abubuwan
daya kirkira aduniya.
Kuma wannan applications da
ake amfani dashi amatsayin
gwaji ga yara, da masu wannan
bangare, waya kirkiri wannan
application din?
amsarka babu ce kawai, domin
baka san waya kirkire shi ba.
Mutane daya ne suka kirkire shi,
kuma ma bam-banta kasa balle
gari, domin su kara jawo masoya
shafinsu na kowanne bangare.
Kuma idan mutum yana bin irin
wadannan applications din to
wataran zai yi gamo da na
Torrent website, wanda saidai ka
canza waya, amma wannan ta
mutu. Saboda Virus mai karfin
gaske zata gamu dashi, nan take
ya kashe maka waya.
0 Replies 1728 Views 0 Bookmarks
topics posts

* Abbaatee1 Forum
fav Bookmarks

* Abbaatee1


Download PRODIGITS Android APP